Isa ga babban shafi
EAC

Congo ta zama mamba a Kungiyar Gabashin Afrika

Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta zama cikakkiyar mamba a Kungiyar Kasashen Gabashin Afrika ta EAC wadda ke gudanar da hada-hadar kasuwancin bai-daya a tsakanin mambobinta da kuma bai wa al’ummar yankin damar zirga-zirgarsu kai tsaye cikin kasashen yankin.

Tutar Kungiyar Gabashin Afrika ta EAC
Tutar Kungiyar Gabashin Afrika ta EAC EAC
Talla

Kungiyar ta EAC mai shalkata a birnin Arusha na Tanzania, yanzu ta fadada zuwa kasashe 7 da suka hada da Burundi da Kenya da Rwanda da Tanzania da Sudan ta Kudu da Uganda, sai kuma Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da ta zama bakuwa a kungiyar.

Shugaban Kungiyar ta EAC kuma shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta, shi ne ya sanar da karbar Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a matsayin sabuwar mamba, matakin da ya bayyana da wani sabon tarihi.

Yanzu haka wannan kungiya ta kara samun fadin kasa wanda ya taso daga Tekun India har zuwa can Tekun Atlantic, abin da ya sa kasashen kungiyar suka kara samun damar damawa da su a fagen goyayyar kasuwanci a nahiyar Afrika.

Tun dai shekara ta 2000 ne dai, aka kafa wannan kungiyar, inda ta yi aiki tukuru wajen karfafa hada-hadar kasuwanci ta hanyar cire kudaden fito a tsakanin mambobinta, yayin da a shekara ta 2010, ta assasa kasuwancin bai-daya.

Yanzu haka Jamhuriyar Demokuradiyar Congo mai yawan al’umma miliyan 90 wadda kuma ke da arzikin karkashin kasa, za ta fadada kasuwancin kungiyar  zuwa kusan na mutane miliyan 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.