Isa ga babban shafi

An soma taron shugabanin kasashen gabashin Afirka a Burundi

A yau asabar ne shugabannin kasashen gabashin Afirka suka je kasar Burundi domin gudanar da wani taron yankin da zai tattauna rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Shugaban DRCongo  Félix Tshisekedi, a Burundi  Félix Tshisekedi,
Shugaban DRCongo Félix Tshisekedi, a Burundi Félix Tshisekedi, AFP - TCHANDROU NITANGA
Talla

Kungiyar kasashen gabashin Afirka da ke jagorantar kokarin shiga tsakani domin kawo karshen fadace-fadacen da ake fama da shi a gabashin kasar da ke tsakiyar Afrika ta tsakiya ne ke karbar bakuncin taron a cibiyar tattalin arzikin kasar Burundi a Bujumbura.

Shugabanin za su mayar da hankali a kan tattalin Arziki, tsaro a gabashin Dimokaradiyyar Congo.

 Shugaba Paul Kagame na Rwanda, wanda ake zargi da marawa kungiyoyin 'yan tawaye baya a gabashin DRC, yana cikin wadanda suka halarci wannan taro, a wannan  ziyararsa ta farko a Burundi tun shekara ta 2013 lokacin da ya halarci bikin samun 'yancin kai.

Kasashen biyu da ke makwabtaka da yankin manyan tafkuna na tsakiyar Afirka sun dade suna da alaka mai zafi, inda kowannensu ke zargin juna da yin katsalandan a harakokin cikin gidansu.

A shekarar 2020, Kagame ya bukaci sabon zababben shugaban kasar Burundi na lokacin Evariste Ndayishimiye da ya sake kulla huldar diflomasiyya amma aka ki amincewa da matakin da ya dauka a lokacin.

Burundi musamman ta zargi Rwanda da baiwa wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin mafaka a shekarar 2015 da ya jefa kasar cikin tashin hankali.

Fadar shugaban kasar ta Burundi ta wallafa hotunan isar Kagame a birnin da kuma wasu shugabannin kasashen da suka hada da shugaban kasar Kenya William Ruto, da tsohon shugaban Uganda Yoweri Museveni, da Samia Suluhu Hassan ta Tanzania.

Wani jami'in fadar shugaban kasar Congo ya fada jiya Juma'a cewa shugaban kasar Felix Tshisekedi zai je taron.

Ana gudanar da taron ne jim kadan bayan ziyarar da Fafaroma Francis ya kai birnin Kinshasa, inda ya gana da wadanda rikicin ya rutsa da su, ya kuma yi Allah wadai da ta'addancin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.