Isa ga babban shafi

Rwanda ta zargi Amurka da ruruta rikicin Congo

Ministan harkokin wajen kasar Ruwanda ya zargi kasashen duniya da ‘kara tsananta rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da ke fama da kungiyoyin masu dauke da makamai, bayan da Amurka ta bukaci Kigali da ta dakatar da duk wani goyon bayan da aka ce tana baiwa ‘yan tawayen.

Manzo na musamman kan sauyin yanayi na Amurka, John Kerry tare da shugaban Rwanda, Paul Kagame a Kigali, ranar 15, ga Oktoban 2016
Manzo na musamman kan sauyin yanayi na Amurka, John Kerry tare da shugaban Rwanda, Paul Kagame a Kigali, ranar 15, ga Oktoban 2016 REUTERS/James Akena
Talla

A wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame a ranar Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken "ya bayyana karara cewa dole ne a kawo karshen duk wani goyon bayan waje ga kungiyoyin masu dauke da makama a kasar, ciki har da tallafin da Rwanda ke bawa M23".

Fadan da ake gwabzawa a gabashin Congo tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen M23, tsohuwar kungiyar 'yan tawayen Tutsi, ya kara tada jijiyoyin wuya da makwabciyarta Rwanda, wadda kasar ke zargi da karfafa gwiwar mayakan.

A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, Ministan Harkokin Wajen Rwanda, Vincent Biruta, ya tabbatar da cewa Paul Kagame da Anthony Blinken "sun yi musayar ra'ayi duk da cewa akwai banbancin ra’ayin kuma".

Kasar Rwanda ta sha dora alhakin rikicin gabashin Congo a kan mahukuntan birnin Kinshasa, inda ta kuma zargi kasashen duniya da rufe ido kan yadda ake ganin suna goyon bayan kungiyar ‘yan tawayen Hutu ta Rwanda, wadanda wasu daga cikinsu ke da hannu a rikicin 1994.

Wani taron kolin da aka gudanar a ranar 23 ga watan Nuwamba a Angola ya ba da umarnin tsagaita bude wuta tare da janyewar 'yan tawaye daga wuraren da suka kama a watannin baya-bayan nan, sai dai kawo yanzu ba a mutunta yarjejeniyar ba.

Bayan tsagaita bude wuta na kwanaki 5, an sake samun barkewar wani kazamin fada a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a cikin makon jiya tsakanin 'yan kungiyar M23 da sojojin Congo, wanda gwamnati ta zargi 'yan tawayen da kashe fararen hula kusan 300.

Sai dai M23 ta yi watsi da wadannan zarge-zargen tare da yin kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.