Isa ga babban shafi

Amurka ta damu da rahoton hannun Rwanda a taimakon 'yan tawayen M23- Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurka ta damu da rahotanni masu sahihanci da ke cewa Rwanda na goyon bayan ‘yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Anthony Blinken yayin ziyararsa a birnin Kinshasa.
Anthony Blinken yayin ziyararsa a birnin Kinshasa. REUTERS - POOL
Talla

Sake bayyanar kungiyar ‘yan tawaye ta M23 a gabashin Congo mai fama da tashin hankali ya kara ta’azzara rikicin da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna inda Kinshasa ta zargi Kigali da goyon bayan ‘yan tawayen.

Rwanda dai ta musanta zargin, wanda ya kai ga shiga tsakanin kungiyar kasashen gabashin Afrika don sasanta Rwandan da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo lamarin da ya kai ga cimma yarjejeniyar tilastawa mayakan na M23 ajje makamai tare da janyewa daga yankin da suka yi tunga a Congo.

Sai dai a baya-bayan wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana hannun Rwanda a taimakawa kungiyar 'yan tawayen ta M23.

Bayan ziyarar kwana guda a Congo Antony Blinken na shirin karkarewa da Rwanda inda tuni ya fara aikewa da bacin ran Amurka kan hannun kasar a taimakon ayyukan ta'addanci a makwabiyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.