Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta zargi 'yan tawaye da kashe 'yan kasar China 9

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta zargi babbar kungiyar ‘yan tawayen kasar ta CPC da kashe wasu ‘yan kasar China 9 da ke aikin hakar zinare a watan Maris. 

Wasu dakarun jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2021
Wasu dakarun jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2021 AFP - FLORENT VERGNES
Talla

Tun a watan na jiya ‘yan tawayen suka musanta zargin, tare da dora alhakin kashe Sinawan akan sojojin hayar Rasha na kamfanin Wagner da ke bai wa wasu kamfonin hakar ma’adanin na Zinare daga Rashan tsaro. 

Tun a shekarar 2018, kamfanin sojojin haya na Wagner ya girke daruruwan dakarunsa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda kuma aka karo wasu a 2020, domin taimakawa gwamnati wajen dakile ‘yan tawayen da suka sha alwashin yi wa shugaba Archange Touadera juyin mulki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.