Isa ga babban shafi

'Yan tawaye sun kashe sojoji 6 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

‘Yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun kashe sojoji 6 a wani hari da suka kai a kudu maso gabashin kasar inda aka shafe shekaru ana gwabza yakin basasa.

Sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. AFP - FLORENT VERGNES
Talla

Wani dan majalisar dokokin yankin Gabin Mboli Fouele ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar da karfe hudu na safe ne ‘yan tawayen suka kai hari a garin Nzako da ke kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai tazarar kilomita 700 daga birnin Bangui babban birnin kasar.

Dan majalisar ya kara da cewar, baya ga sojoji 6 da suka mutu, an kuma kashe mayakan 'yan tawaye uku.

Fouele ya ce kungiyar mayakan masu fafutukar neman sauyi da aka kafa a watan Disamban shekarar 2020 domin hambarar da shugaba Faustin Archange Touadera, ne suka kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.