Isa ga babban shafi

An sake dage shari'ar laifukan yaki a Jamhuriyar Afirka

An dage sauraron shari'ar farko da aka dade ana jira a karkashin kotun da aka kafa domin hukunta laifukan yaki a rikicin da ya tagayyara al’ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

wasu 'ya'yan kungiyar. mayakan sa-kai na 3R da ake tuhuma da aikata laifukan yaki a rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
wasu 'ya'yan kungiyar. mayakan sa-kai na 3R da ake tuhuma da aikata laifukan yaki a rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. © REUTERS/ Leger Kokpakpa
Talla

Karo na biyu kenan da ake dage lokacin fara sauraron shari’ar a cikin watan Afrilun nan.

Lauyan daya daga cikin wadanda ake tuhuma da aikata laifukan yakin, Paul Yakola, ya shaida wa manema labarai cewa, masu kare wadanda ake tuhuma sun bukaci kotun da ta dage zaman ne saboda rashin cikakken shirin da suka y ikan shari’ar.

Sai dai dan sanda mai shigar da kara Alain Wabibikaye ya ce ya yi imanin hakan wata dabara ce ta jinkirta fara shari’a kan tuhume-tuhumen aikata munanan laifukan yakin da aka dade ana jiran gani.

A ranar 19 ga watan Afrilu aka fara dage zaman sauraron kararrakin, lokacin da lauyoyin wadanda ake kara suka kauracewa zaman kotun.

Shari’ar dai na da alaka da kisan kiyashin da aka yi wa farar hula 46 a kauyukan Koundjili da Lemouna na arewacin kasar ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a watan Mayun shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.