Isa ga babban shafi

Afirka ta Tsakiya ta bukaci a mika mata wani tsohon Kwamandan Seleka

Mai shigar da kara na gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya bukaci kotun duniya da ke Hague, ta danka masa wani tsohon Kwamandan kungiyar ‘yan tawayen Seleka mai suna Mahamat Said domin yi ma shi shari’a a birniin Bangui bisa zarge-zargen aikata laifukan yaki tsakanin 2012 zuwa 2013.

Yan Tawayen Seleka na Afirka ta Tsakiya
Yan Tawayen Seleka na Afirka ta Tsakiya REUTERS/Joe Penney
Talla

A cikin shekarar bara ne dai aka kama tsohon madugun ‘yan tawayen, kuma an tsaya fara yi ma shi shari’a ne a ranar 26 ga watan satumbar wannan shekara ta 2022 a Hague, yayin da mahukuntan Bangui ke fatan ganin an tasa keyarsa zuwa gida.

Kasar ta Afirka ta Tsakiya ta fuskanci tawaye ne tun bayan juyin mulkin da Shugaba Bozize yayi a shekara ta 2003 tare da da samun goyan bayan kasar Chadi.

Yan Tawyen Seleka na kasar Afirka ta Tsakiya
Yan Tawyen Seleka na kasar Afirka ta Tsakiya REUTERS/Goran Tomasevic

Sai dai a shekara ta 2012,al'amura sun dagule,tun bayan da aka samu hadakar kungiyoyim tawaye dauke da makamai a karkashin kungiyar Seleka,wacce ake zargin da dama daga cikin shugabaninta da aikata laifukan yaki kama daga 2012 zuwa 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.