Isa ga babban shafi

Sadio Mane gwarzon dan wasan kwallon kafar Afirka na shekarar 2022

A jiya alhamis aka gudanar da bikin tattance gwarazen 'yan wasan kwallon kafar Afirka tare da  bayar da kyaututuka na Awards ga yan wasan daga hukumar kwallon kafar Afirka ta Caf a Rabat na kasar Morocco.

Sadio Mane gwarzon dan wasan shekarar 2022 yayin bikin da ya gudana a Rabat na kasar Morocco
Sadio Mane gwarzon dan wasan shekarar 2022 yayin bikin da ya gudana a Rabat na kasar Morocco REUTERS - ABDELHAK BALHAKI
Talla

Wannan dai ne karo na biyu da  Sadio Mane dan wasan  Senegal ke lashe irin wannan kyauta, baya ga shekara ta  2019.

Indan aka yi tuni a shekaru 2020 da 2021  ba  a gudanar da irin wannan biki ba sabili da cutar Covid 19.

An bayyana dan wasan a matsayin dan wasan da ya taka muhimiyar rawa yayin gasar cin kofin Afrika a watan Fabrairu shekarar 2022 tareda kungiyar kwallon kafar kasar sa Sanegal, shine dan wasan da ya zura kwallon da ta taimakawa kungiyar kasar sa Senegal samun kujerar lashe gasar yayin fafatawa da Masar a wasar karshe.

Sadio Mane mai shekaru 30, ba a jima ba da wannan dan wasa ya kulla kwantragi da kungiyar Bayern Munich bayan raba gari da kungiyar sa ta Liverpool dake Ingila.

Da samu wannan kyauta, Sadio Mane ya zarce tsohon abokin tafiyar sa na kungiyar Liverpool  Mohammed Salah da Eadouard Mendy  dan kasar Senegal mai tsaron  gida a kungiyar Chelsea.

Tarihin ya nuna mana cewa Sadio Mane da farko ya kasance da kungiyar Metz ta kasar Faransa, daga bisani ya tsallaka zuwa kungiyar Rb Salsbourg, kana kungiyar Southampton, sai Liverpool, kafi wannan ya kula kwantragi da kungiyar  Bayern Munich.

Mane da zuwan sa kungiyar ta Bayern  Munich ya soma haskawa ,inda  sabuwar kungiyar ta sa ta samu nasara yayin da ta yi tattaki zuwa Amurka,yayin fafatawa da kungiyar  DC United ta kuma lallasa ta da ci 6 da 2,a wannan wasa Sadio Mane ya zuwa kwallo a ragar kungiyar ta DC.

Bangaren masu horarwa ,Aliou Cisse mai horar da kungiyar kwallon kafar Senegal ne aka zaba  a matsayin mai horar  da ya fi nuna bajinta a shekara.

Yar wasar Najeriya Asisat Oshoal dake taka leda a  kungiyar Barcelona ce ta lashe  kyautar bangaren mata,hakan kuma ne karo na biyar da  da yar wasar Najeriya ke kai irin wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.