Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire- MDD

'Yan gudun hijirar Cote d'Ivoire za su rasa kariyar da su ke samu- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akasarin 'yan gudun hijirar Cote d’Ivoire da su ke zama a kasashen da ke makwabtaka da kasar za su rasa kariyar da su ke da ita a shekara mai zuwa.

Wasu 'yan gudun hijirar Cote d'Ivoire da suka sami mafaka a Libya.
Wasu 'yan gudun hijirar Cote d'Ivoire da suka sami mafaka a Libya. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Wannan ya biyo bayan sanya hannun da kasar Cote d‘Ivoire da kasashen da suka karbi 'yan gudun hijirar suka yi tare da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar domin kawo karshen gudun hijirar.

Raouf Mazou, mataimakin kwamishinan kula da 'yan gudun hijirar ya ce sakamakon nazarin da aka yi akan kasar ta Cote d’Ivoire da yadda al’amura suka sauya, yanzu babu dalilin da wadancan mutane za su ci gaba da zama 'yan gudun hijira.

A shekarar 2010 rikicin siyasar kasar bayan faduwar shugaba Laurent Gbagbo zabe, ya yi sanadiyyar kashe mutane sama da dubu 3 da kuma haifar 'yan gudun hijirar da suka samu mafaka a wasu kasashen da ke makwabta da Cote d’Ivoire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.