Isa ga babban shafi
WHO-'Yan gudun hijira

'Yan gudun hijira sun karu duk da tsanantar Korona-WHO

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsanantar tasirin annobar Korona ba ta hana karuwar adadin miliyoyin mutanen da yaki da sauran tashe-tashen hankula da masifu ke tilasta wa yin gudun hijira ba, ta yadda a wannan karon adadin ya fi na kowane lokaci muni cikin shekaru 10.

Wasu 'yan gudun hijira da suka guje wa tashin hankali daga kasarsu
Wasu 'yan gudun hijira da suka guje wa tashin hankali daga kasarsu AP
Talla

Cikin sabon rahoton da ta fitar, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce, yanzu haka adadin mutanen da suka tagayyara bayan rasa muhallansu sakamakon yake-yake, tashin hankali da rikice-rikice da zalunci ya kai miliyan 82 da dubu 400 a fadin duniya.

Rahoton  ya nuna cewar, yawan mutanen da ke gudun hijira a duniya ya ninka cikin shekaru 10 kacal, daga mutane miliyan 40 a shekarar 2011 zuwa miliyan 82 da dubu 400 a karshen shekarar 2020, wadanda mafi akasarinsu ke sansanonin da aka kafa a kasashensu na asali.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yake-yaken da ake yi a kasashen Syria da Afghanistan da Somalia da Yemen a matsayin dalilan da ke kan gaba wajen janyowa karuwar miliyoyin ‘yan gudun hijirar a sassan duniya, yayin da kuma sabbin tashe-tashen hankulan kasashen Habasha da Mozambique ke barazanar sake dagula lamurra.

Kididdigar Majalisar ta kuma bayyana cewar, yanzu haka akwai ‘yan kasar Venezuela kadai kusan miliyan 4 da suka tsere daga kasashensu saboda rikicin siyasa da na tattalin arziki, wadanda har yanzu hukumomi ba su yi musu rijistar zama ‘yan gudun hijira ba, yayin da kuma a gefe guda adadin Falasdinawa da suka tsere daga yankinsu ya kai miliyan 5 da dubu 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.