Isa ga babban shafi
Najeriya - gudun hijira

'Yan Najeriya dubu 322 na gudan hijira a kasashe makwabta - Gwamnati

Ministar agaji da ci gaban al'umma a Najeriya, Sadiya Umar Farouq, ta ce 'yan Najeriya 322,000 ne ke gudun hijira a maƙotan ƙasashe, wato Nijar, Kamaru da kuma Chadi.

'Yan gudun hijirar Najeriya dake sansanin Minawawo na kasar Kamaru.
'Yan gudun hijirar Najeriya dake sansanin Minawawo na kasar Kamaru. Reinnier KAZE / AFP
Talla

Hajiya Sadiya ta bayyana hakan ne jiya Asabar a Abuja yayin da take sauka daga muƙamin shugabancin hukumar kula da 'yan gudun hijira ƙarƙashin tawagar Technical Working Group (TWG), inda ta miƙa wa Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim muƙamin.

Jaridar Daliy Trust da ake wallafa wa a Najeriya ta ruwaito cewa an miƙa mulkin ne yayin da hukumomi ke ƙoƙarin yi wa 'yan gudun hijirar Najeriya da ke zaune a Kamaru da Nijar da Chadi rajista.

Uwargida Sadiya, tace kimanin ‘yan Najeriya 186,957 ke zaman mafaka a Nijar, 118,409 a Kamaru sai kuma 16,634 a Chadi.

Ta ƙara da cewa gwamnatin Najeriya na shirin ƙulla yarjejeniya da Nijar da Chadi game da dawo da mutanen gida kamar yadda ta ƙulla da Kamaru.

Yaƙin Boko Haram da kuma hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da muatne sukayi sanadiyar tserewar mutane daga muhallansu a arewacin Najeriya, inda dubbai ke tsallakawa maƙotan ƙasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.