Najeriya ta fara shirin kwashe ‘yan kasar ta dake gudun hijira a Kamaru
Gwamnatin Najeriya ta fara shirin kwashe ‘yan kasar ta dake gudun hijira a Kamaru domin mayar dasu gida, bayan da jami’an kasashen 2 suka tattauna kan shirin karkashin Majalisar Dinkin Duniya a birnin Marwa.
Wallafawa ranar:
Kwamishinan kula da ‘yan gudun hijira a Najeriya Sanata Bashir Garba Lado yace taron ya biyo bayan umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganin an kwashe ‘yan gudun hijirar dake zama a Kamaru cikin gaggawa.
Takwaransa dake Kamaru Tai Hassan Ejibunu ya yaba da tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin uku wanda yace za’ayi aikin ne wajen kwashe bakin dake bukatar komawa gida.
Taron yace shirin dawo da yan gudun hijirar ya kunshi samar musu da matsuguni, inda za’a basu gidaje masu dakuna bibbiyu a wasu jihohin kasar dake kusa da cibiyoyin kula da lafiya da makarantu da wuraren koyon sana’oi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu