Isa ga babban shafi
NIJAR-TA'ADDANCI

Nijar zata mayar da 'Yan gudun hijirar Najeriya gida

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed yace shi da gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum na shirin mayar da Yan gudun hijirar Najeriya sama da dubu 130 gida nan da karshen wannan shekarar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Nijar Bazoum Mohammed
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Nijar Bazoum Mohammed © Niger Presidency
Talla

Yayin da yake ganawa da manema labarai bayan taron G5 Sahel da ya gudana a Paris tare da shugaban Faransa Emmanuel Macron, Bazoum yace su sanya wa’adin watan Nuwamba zuwa Disamba domin kwashe daukacin Yan gudun hijirar Najeriya dake Jihar Diffa zuwa gida.

Janhuriyar Nijar ta tsugunar da dubban an gudun hijirar Najeriya da suka gudu daga garuruwan su saboda hare haren kungiyar book haram wadda ta kwashe sama da shekaru 10 tana kai munanan hare hare a yankunan arewacin Najeriya, matsalar da ta fadada zuwa kasashen Nijar da Chadi da kuma Kamaru.

Shugaba Emmanuel Macron yana tarbar shugaban Nijar Bazoum Mohammed a Paris
Shugaba Emmanuel Macron yana tarbar shugaban Nijar Bazoum Mohammed a Paris © Niger Presidency

Jihar Borno tafi jin radadin rikicin wanda yayi sanadiyar kasha mutane akalla dubu 40 da kuma raba sama da miliyan 2 daga muhallin su.

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum na ta kokarin mayar da Yan gudun hijira zuwa garuruwan su domin sake tsugunar da su amma Karin hare haren book haram na yiwa shirin zagon kasa.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed a Paris
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed a Paris © Niger Presidency

Ita ma Jamhuriyar Nijar na fama da yake yake kala biyu da suka hada da na boko haram da kuma Yan bindigar Mali dake ikrarin jihad, wadanda ke tsallaka iyaka suna kai hari cikin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla Yan gudun hijirar Najeriya dubu 300 ke Yankin Diffa wadda ita ma take fama da hare haren mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.