Isa ga babban shafi
ZABEN-ZAMBIA

Yau za'a rantsar da sabon shugaban kasar Zambia Hichilema

Yau ake saran rantsar da zababben shugaban Zambia Hakainde Hichilema a matsayin sabon shugaban kasa, sakamakon nasarar da ya samu a zaben da ya gudana inda ya kada shugaba mai ci Edgar Lungu.

Zababben shugaban kasar Zambia  Hakainde Hichilema
Zababben shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema © Tsvangirayi Mukwazhi/AP
Talla

Tuni nasarar Hichilema ta karfafa wasu ‘Yan adawa a Afirka inda suke ganin cewar, jajircewa na iya basu damar samun nasara, ganin yadda zababben shugaban kasar na Zambia yayi takara har sau 5 kafin samun nasara a wannan lokacin.

Zababben shugaban wanda ya fuskanci cin zarafi iri-iri a hannun hukumomin Zambia ya sha alwashin kawo sauyi a bangaren dimokiradiyar kasar da kuma tabbacin samar da ‘yanci ga jama’a wajen bayyana abinda suke bukata.

Wani mai goyan bayan Hakainde Hichilema
Wani mai goyan bayan Hakainde Hichilema Patrick Meinhardt AFP

Yayin da yake jawabin samun nasara, Hichilema mai shekaru 59 yayi alkawarin zama shugaban daukacin jama’ar Zambia ba tare da nuna banbanci tsakanin al’ummar kasar ba.

A jawabin da yayi bayan bayyana sakamakon zaben, shugaba mai barin gado Edgar Lungu ya godewa al’ummar kasar da suka bashi damar jagorancin su, abinda yace zai ci gaba da tunawa a rayuwar sa.

Hukumar zabe ta bayyana cewar Hichilema ya samu kuri’u miliyan 2 da dubu 810,757, yayin da shugaba Lungu ya samu kuri’u miliyan guda da dubu 814,201.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.