Isa ga babban shafi

Hukumar zaben Zambia ta soma fitar da sakamakon zaben kasar

Hukumar zaben kasar Zambia na ci gaba da tattara sakamakon zaben Shugaban kasar da ya gudana ranar alhamis da ta gabata, hasashen farko na nuni cewa jagoran yan adawa kuma dan takara a zaben Hikaine Hichilema ke kan gaba, yayinda bangaren Shugaban kasar mai ci Edgar Lungu suke ci gaba da nuna damuwa dangane da sahihanci wannan zabe.

Hukumar zaben Zambia
Hukumar zaben Zambia MARCO LONGARI AFP
Talla

Daga cikin ruhunan zabe  156,hukumar zaben kasar ta bayar da sakamakon ruhuna 62 wanda hakan ke baiwa jagoran yan adawa yawan kuri’u  milyan daya da dubu 24 da 212,yayinda Shugaban kasar Edgar Lungu mai shekaru 64 ya tashi da kuri’u dubu 526.523.

Wasu daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma dan takara Edgar Lungu
Wasu daga cikin magoya bayan Shugaban kasar kuma dan takara Edgar Lungu Patrick Meinhardt AFP

Hankula dai sun fi karkata kan shugaba Edgar Lungu da babban abokin hamayyarsa kuma fitaccen attajrin kasar ta Zambia Hakainde Hichilema, wanda ya samu gagarumin kaso a zaben baya da aka gudanar.

A karo na shida kenan da Hichilema ke fitowa takara a zaben shugaban kasar Zambia, kuma a wannan karo yana samun goyon bayan jam’iyyu akalla 10 da suka yi hadaka da shi.

Edgar Lungu Shugaban kasar Zambia
Edgar Lungu Shugaban kasar Zambia Gianluigi Guercia AFP/File

A  zaben da aka gudanar a 2016, da kkyar da jibin goshi shugaba Lungu mai shekaru 64, ya bai wa Hichilema ratar kuri’u dubu 100, abin da ke nuni da cewa, ko a bana ma dai, sai  ya yi da gaske kafin ya kai labari.

Sai dai shugaba Lungu ya yi kurin cewa, a wannan shekara ta 2021, zai bai wa Hichilema ratar kuri’u dubu 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.