Yan adawa a Zambia na zargin gwamnati da hana jagoranta isa Copperbelt
Jagoran yan adawa a Zambia Hakainde Hichilema dake neman kujerar shugabancin kasar karo na shida ya sanar da magoya bayan sa cewa an hana shi ya gudanar da yakin neman zabe a lardin tsakiya na Copperbelt.
Wallafawa ranar:
Jagoran yan adawa ya karasa da cewa ,an sheida masa cewa shugaban kasar na ziyarar yankin a lokacin ,sabili da haka ba zai iya isa lardin ba yanzu haka,lamarin da ya kai ga soke izinin da hukuma ta ba shi na gita sarrarin samaniya na yankin a lokacin.
Sai dai mai magana da yahun jagoran yan adawa na kasar y ace jam’iyyar su ta yi watsi da wannan mataki.
Ranar alhamis na mako mai kamawa ne yan kasar za su sake zabar jam’iyyar da za ta shugabancin kasar,zaben da yan adawa ke sa ran wannan karo za su samu galaba fiye da shekarun da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu