Isa ga babban shafi
Zambia

Zambia ta sanar da makokin makwanni 3 kan mutuwar Kenneth Kaunda

Gwamnatin Zambia ta sanar da mutuwar tsohon shugaban kasar Kenneth Kaunda yau alhamis yana da shekaru 97 a duniya. Sakataren Majalisar ministocin kasar Simon Miti ya sanar da mutuwar a jawabin da ya yiwa al’ummar kasar.

Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda, yayin gwgwarmayarsa a 1978.
Tsohon shugaban kasar Zambia Kenneth Kaunda, yayin gwgwarmayarsa a 1978. AFP - -
Talla

Sanarwar gwamnatin Zambia ta ce tsohon shugaban kasa Kenneth Kaunda ya rasu ne a asibitin sojin kasar da misalin karfe 2.30 agogon Zambia inda ake kula da shi saboda cutar da ke da nasaba da numfashi.

Sakataren Majalisar ministocin Simon Miti ya sanar da zaman makoki na makwanni 3 wanda zai kunshi rage tutar kasar da katse duk wasu bukukuwan da aka shirya.

Shugaban kasa Edgar Lungu ya bayyana kaduwar sa da mutuwar, inda yake cewa Kaunda ya rasu lokacin da ba suyi zato ba, yayin da ya bayyana shi a matsayin gwarzon Afirka.

Kenneth Kaunda ya jagoranci kasar Zambia na shekaru 27 tun bayan samun ‚yancin kan kasar daga watan Oktobar shekarar 1964 daga Turawan mulkin Birtaniya.

Shugaban da ake yiwa lakabi da KKK ya jagoranci jam’iyyar masu kishin kasa ta United National Independence Party UNIP wadda tayi gwagwarmayar neman yanci.

Lokacin da yake karagar mulki ya taimakawa kungiyoyi da dama dake fafutukar neman yancin kai a kasashen dake yankin kudancin Afirka cikin su harda kungiyar ANC ta Afirka ta Kudu wadda ta rikide ta zama Jam’iyyar ANC ta Nelson Mandela.

Wasu mutane sun yiwa Kaunda sunan ‘Shugaba Ghandi na Afirka‘ saboda fafutukar sa na neman yanci ba tare da tashin hankali ba.

A wani lokaci farin jinin sa ya ragu lokacin da ya soke jam’iyyun adawa, abinda ya sa aka dinga sukar sa a gida da waje.

A shekarar 1991 ya sauka daga mulki lokacin da ya mika ragamar tafiyar da kasar ga shugaba Frederick Chiluba bayan ya sha kayen zabe, kafin daga bisani ya dawo da kimar sa a idan duniya wajen sasanta rikicin cikin gida a kasashen Zimbabwe da Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.