Isa ga babban shafi

IMF ta bukaci Zambia ta sauya manufofin tattalin arzikinta

Asusun bada lamuni na duniya ya ce dole sai Zambia ta sake tsara manufofin tattalin arzikinta don iya ci gaba da biyan basukan da ta karba, bayan da kasar, mai arzikin jan gaci ta nemi rance daga asusun, don aiwatar da sauye sauyenta.

Edgard Lungu, shugaban Zambia
Edgard Lungu, shugaban Zambia lt.jpeg
Talla

Zambia, wacce basukan da ta ci suka tashi zuwa kusan dala biliyan 12 a wannan shekarar, ta aike da bukata neman rance daga IMF a ranar Talatar da ta gabata.

Amma a yayin da yake karkare wata ziyarar da ya kai Lusaka, babban birnin Zambia, Daraktan asusun bada lamuni na duniya reshen Afrika, Abebe Aemro Selassie ya ce duba da kalubalen tattalin arziki da kasar ke fuskanta, akwai bukatar a sake tsara manufofi don samar da mafita mai dorewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.