Isa ga babban shafi
Zambia

An dakatar da ‘yan Majalisu 48 a Zambia

Shugaban Majalisar dokokin Zambia ya dakatar da ‘yan Majalisu 48 na babbar jam’iyyar adawar kasar, sakamakon kauracewa sauraron jawabin da shugaba Edgar Lungu, ya gabatar a gaban majalisar.

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu GIANLUIGI GUERCIA / AFP
Talla

Shugaban Majalisar Patrick Matibini," Ya ce bisa karfin ikon da doka ta ba shi ne, ya yi amfani da damar wajen dakatar da ‘yan Majalisun daga bakin aiki na tsawon wata guda.

Har ila yau kakakin majalisar ya bukaci ‘yan majalisar da su yi murabus baki daya idan basu san cewa akwai halatacciyar gwamnati da aka zaba ba ta hanyar demokradiya a kasar ba.

Bugu da kari hukunci ya haramtawa ‘yan Majalisun tsoma kafa a harabar majalisar tare da soke albashinsu na tsawon lokacin da aka dakatar da su.

A cikin watan Maris da ya gabata ne, 'yan Majalisun daga jam’iyar UPND mai adawa suka ki halartar jawabin da shugaba Lungu ya gabatar a zauren majalisar dokokin, sakamakon nuna rashin amincewa da halacin zaben da aka yi masa a watan Agustan 2016, wanda suka yi zargin cewa ya tafka magudi a cikinsa.

A cikin wani sako ta shafin Facebook, Jam’iyar adawar ta UPND ta yi tir da zargin da cewa ba shi da tushe balantana makama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.