Isa ga babban shafi
Zaben Zambia

'Yan Zambia sama da miliyan 7 na zaben sabon shugaban kasa

Sama da mutane milyan 7 ke kada kuri’unsu yau Alhamis don zaben sabon shugaban kasa a Zambia, inda ‘yan takara 16 ke karawa da juna, ciki har da shugaba mai-ci Edgar Lungu.

Magoya bayan Shugaban Zambia mai barin gado Edgar Lungu a Lusaka a ranar 11 ga Agusta, 2021.
Magoya bayan Shugaban Zambia mai barin gado Edgar Lungu a Lusaka a ranar 11 ga Agusta, 2021. Patrick Meinhardt AFP
Talla

Hankula dai sun fi karkata kan shugaba Edgar Lungu da babban abokin hamayyarsa kuma fitaccen attajrin kasar ta Zambia Hakainde Hichilema, wanda ya samu gagarumin kaso a zaben baya da aka gudanar.

A karo na shida kenan da Hichilema ke fitowa takara a zaben shugaban kasar Zambia, kuma a wannan karo yana samun goyon bayan jam’iyyu akalla 10 da suka yi hadaka da shi.

A  zaben da aka gudanar a 2016, da kkyar da jibin goshi shugaba Lungu mai shekaru 64, ya bai wa Hichilema ratar kuri’u dubu 100, abin da ke nuni da cewa, ko a bana ma dai, sai  ya yi da gaske kafin ya kai labari.

Sai dai shugaba Lungu ya yi kurin cewa, a wannan shekara ta 2021, zai bai wa Hichilema ratar kuri’u dubu 500.

Shugaban mai ci dai na shan suka daga ‘yan kasar musamman saboda yadda tattalin arzikinsu ya fuskanci mummunan koma baya a karakshin gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.