Isa ga babban shafi
Zambia-Kaunda

An kammala jana'izar tsohon shugaban Zambia Kenneth Kaunda

An kammala jana’izar tsohon shugaban kasar Zambia wanda ya jagoranci karbo 'yancin kasar, Kenneth Kaunda inda aka birne shi a makabartar da ake birne manyan shugabannin kasar duk da kin amincewar hakan daga ‘yan uwansa.

Jana'izar Kenneth Kaunda.
Jana'izar Kenneth Kaunda. AFP - -
Talla

Gabanin fara fara jana'izar alkalin babbar kotun kasar, Wilfred Muma ya ki amincewa da bukatar a birne shi a gonarsa ya na mai cewa Kaunda na daga cikin muhimman mutanen da ake alfahari da su a kasar, don haka za a binne shi a inda ya dace.

Hakan ta sanya gwamnatin kasar ta bayar da umarnin gudanar da bikin jana'izar a Embassy Park, wata makabarta ta alfarma da aka kebewa shugabannin kasar.

Wasu daga cikin dangin marigayin dai sun so a birne shi a wata gonarsa kusa da inda aka birne matarsa Betty.

Dubban mutane ne a kasar ke bayyana alhinin mutuwar Kaunda da ya koma ga mahaliccinsa yana da shekaru 97 a Duniya, wadanda ke bayyana shi a matsayin mai fafutuka dan gwagwarmaya kuma malami wanda ya kamata ayi koyi da shi.

Shugaba Edgar Lungu ya bayyana ranar haihuwar Kaunda, 28 ga Afrilu, a matsayin ranar hutu don girmama shugaban kasar na farko kuma dan fafatuka wanda ya yi gwagwarmayar kwato 'yancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.