Hakainde Hichlema, ya lashe zaben shugabancin Zambia
Dan takarar adawa a zaben shugabancin kasar Zambia Hakainde Hichlema, ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar alhamis da ta gabata kamar dai yadda alkalumman hukumar zabe suka nuna.
Wallafawa ranar:
Samarakon mazabu 155 daga cikin 156 da hukumar zaben ta fitar na nuni da cewa Hichilema ya samu kuri’u sama da milyan 2 da dubu 810 da kuri’u 757, yayin da shugaba mai-ci Edagar Lungu ya samu kuri milyan 1 da dubu 814 da 201 a wannan zabe.
Lura da wadannan alkalumma ne shugaban hukumar zaben kasar Esau Chulu ya tabbatar da Hichileme a matsayin zababben shugaban kasar Zambia.
Dan shekaru 59 a duniya, Hichilema wanda shahrarren dan kasuwa ne, ya yi nasarar doke shugaban da ke kan karagar mulkin kasar ne bayan ya tsaya takarar har sau 6, kuma 3 daga cikinsu yana karawa da shugaba Lungu.
A zaben da aka gudanar shekara ta 2016, duka duka an samu ratar kuri’u dubu dari daya ne a tsakanin mutanen biyu, sabanin wannan karo da aka samu tazarar kuri’u kusan milyan daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu