Isa ga babban shafi
Rikicin kasar Libya

Aguila ya bukaci kafa gwamnatin da zata wakilci dukkan bangarorin siyasar Libya

Shugaban majalisar dokokin Libya Aguila Saleh ya yi kira ga Firayinministan rikon kwaryan kasar da ya kafa gwamnatin da za ta wakilci dukkan bangarorin da ke cikin rikicin kasar dake Arewacin Afirka don shawo kan "bambance-bambance" da ake fuskanta.

Shugaban majalisar dokokin Libya mai karfin fada aji Aguila Saleh ya yi kira ga Firayinministan rikon kwaryan kasar da ya kafa gwamnatin da za ta wakilci dukkan bangarorin da ke cikin rikicin kasar.
Shugaban majalisar dokokin Libya mai karfin fada aji Aguila Saleh ya yi kira ga Firayinministan rikon kwaryan kasar da ya kafa gwamnatin da za ta wakilci dukkan bangarorin da ke cikin rikicin kasar. Abdullah DOMA AFP/File
Talla

Kiran na Saleh mai karfin fada aji na zuwa ne kwana daya bayan da Firayinministan rikon kwarya Abdul Hamid Dbeibah ya gabatar da sunayen majalisar ministoci da zasu jagoranci Libya zuwa zabe a watan Disamba mai zuwa.

Wannan ne yasa Kakakin majalisar ke ganin ya kamata Dbeibah ya zabi "kwararrun mutane masu mutunci, daga bangarorin dake rikicin siyasar kasar, domin sasanta kasar da kuma ci gaban gwamnatinsa.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Rabat, bayan tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Morocco Nasser Bourita,  Saleh yace, "Akwai bambance-bambance," da ka iya hana kasar zuwa gaba.

Za’a bayyana sunayen sabbin ministocin da Franministan ya gabatar yayin kada kuri’ar amincewa da su a majalisar.

An zabi Dbeibah ne a farkon wannan watan yayin taron sasanta rikicin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyi, wanda shi ne yunkuri na baya-bayan nan da kasashen duniya sukayi wajen ceto kasar daga rikice-rikicen siyasa na sama da shekaru goma.

Kasar Libiya mai arzikin mai ta fada cikin rikici tun bayan boren da kungiyar tsaro ta NATO ta yi a shekarar 2011 wanda ya yi sanadiyyar hallaka shugaban kasar Moamer Kadhafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.