Isa ga babban shafi
Libya

MDD ta jagoranci kafa sabuwar gwamnati a Libya

Wakilan bangarori masu adawa da juna a Libya sun zabi Abdul Hamid Mohammed Dbeibah a matsayin sabon Fira Ministan gwamnatin rikon kwaryar kasar.

Zauren taron kafa sabuwar gwamnatin Libya a birnin Geneva na kasar Switzerland
Zauren taron kafa sabuwar gwamnatin Libya a birnin Geneva na kasar Switzerland UNITED NATIONS/AFP/File
Talla

Sabon Fira Ministan na Libya ya taba jagorantar kamfanin lura da hada-hadar zuba hannayen jari na kasar, a karkashin gwamnatin tsohon shugaba marigayi Mu’ammar Ghaddafi.

An dai yi zabin ne yayin taron neman kafa gwamnatin hadin gwiwar da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a kasar Switzerland, inda kuma aka kafa majalisar zartaswar gwamnatin rikon kwaryar ta Libya mai manbobi 3, ciki har da Mohammed Younes Menfi a matsayin sabon shugaban kasa.

Gwamnatin rikon kwaryar za ta jagoranci Libya har zuwa ranar 24 ga watan Disambar shekarar nan, lokacin da babban zaben kasar zai gudana.

Kawo yanzu Libya ta shafe kusan shekaru 10 cikin tashin hankali, tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mu’ammar Gaddhafi tare da kashe shi a shekarar 2011.

Rikicin na Libya dai ya kai ga tsagewar kasar zuwa bangaren dake karkashin ikon gwamnati da majalisar dinkin duniya ke marawa baya da kuma bangaren gabashin kasar dake karkashin janar Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.