Isa ga babban shafi
Libya

MDD ta caccaki kasashen da ke sanya hannu a rikicin Libya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da kasashen ketaren da ke sanya hannu a rikicin kasar Libya, abin da ya bayyana a matsayin takaici ganin yadda ake kai makamai da kuma sojojin haya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Lisi Niesner
Talla

Yayin da yake jawabi ga Kwamitin Sulhu wanda ya gudanar da taro na musamman kan rikicin, Guterres ya bayyana damuwa kan yadda ake jibge sojoji kusa da birnin Sirte, wanda ke tsakiyar biranen Tripoli da Bengazi.

Sakataren ya ce rikicin Libya ya shiga wani sabon babi ganin yadda kasashen ketare da dama suka sanya hannu a ciki wajen goyan bayan wani bangare ta hanyar ba su makamai da kuma sojojin haya wadanda suka tsunduma cikin rikicin.

Guterres ya sake bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da girke dakarun soji a kusa da Sirte da ke tsakiyar biranen Tripoli da Benghazi duk da takunkumin hana sayarwa kasar makamai da kuma alkawarin da kasashen ketare suka dauka a taron Berlin na samar da yanayi mai kyau na sasanta rikicin kasar.

Shugaban Kwamitin Sulhu kuma Ministan Harkokin Wajen Jamus,  Heiko Maas ya cacaki kasashen da ke katsalanda cikin rikicin na Libya, inda yake cewa a daidai lokacin da kasashen duniya suka rufe iyakokinsu, sai ga shi ana samun jiragen ruwa da na sama da motoci dauke da makamai da kuma sojin haya na kwarara cikin Libya.

Shi ma Ministan Jamhuriyar Nijar, Kalla Hankurau ya goyi bayan zargin da Sakatare Janar Guterres ya yi wa kasashen duniya, inda yake cewa Libya ba ta bukatar makamai ko sojin haya, sai dai shirin sasanta kasar.

Gwamnatin hadin kan Libya na samun goyan bayan kasar Turkiya wajen yaki da 'Yan tawaye a karkashin Janar Khalifa Haftar, yayin da kasashen Masar da Rasha da Daular Larabawa ke mara wa Janar Haftar baya.

Guterres ya ce rikicin baya bayan nan a Libya ya raba mutane akalla 30,000 da muhallinsu, abin da ya kawo adadin wadanda suka tsere wa muhallin su zuwa sama ad 400,000 yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.