Isa ga babban shafi
Libya-MDD

MDD ta bukaci gaggautar ficewar Sojojin haya da na ketare daga Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta ficewar Sojojin haya da na kasashen ketare daga Libya, ciki har da Sojin Rasha wadanda Majalisar ke zargi da rura wutar rikicin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da zargin hannun Rasha a rura wutar rikicin kasar ta Libya.
Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da zargin hannun Rasha a rura wutar rikicin kasar ta Libya. Getty Images
Talla

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar yayin wani zaman sirri daya gudanar ta bidiyon Internet, ilahirin mambobinsa 15 sun amince da kudirin tilastawa sojojin ketaren su gaggauta ficewa daga kasar wadda ke ci gaba da fuskantar rikici tun bayan hambarar da gwamnatin Moamer Kadhafi a shekarar 2011.

Kwamitin ya ce bisa tanadin yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarori masu rikici da juna suka cimma a ranar 23 ga watan Oktoba babu bukatar sojin haya ko na ketare a cikin kasar.

Kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya jima yana zargin Rasha da rura wutar rikicin Libyan ta hanyar aikewa da Sojin haya wadanda ke dafawa Sojin da ke biyayya ga Khalifa Haftar, matakin da ke matsayin zagon kasa ga amincewar Majalisar da gwamnatin Fayez al Sarraj.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.