Isa ga babban shafi

Bakin Haure 74 sun mutu a tekun Libya

Majalisar dinkin duniya ta ce akalla ‘yan ci rani 74 ne suka mutu a gabar ruwan Libya jiya Alhamis, sakamakon nutsewar jirgin ruwan da suke ciki, yayin da suke kokarin tsallaka tekun meditaraniya domin isa nahiyar Turai.

Irin kwale kwalen da bakin haure ke yawan amfani da shi wajen ketare Meditareniya.
Irin kwale kwalen da bakin haure ke yawan amfani da shi wajen ketare Meditareniya. Photo transmise à RFI par un migrant
Talla

Alkaluma dai sun nuna cewa, daga shekarar bara zuwa ta bana an samu raguwar yawan ‘yan ci ranin dake mutuwa a tekun na Meditaraniya sakamkon raguwar adadin wadanda ke kokarin isa Turai, sai dai adadin ya sake hauhawa a watannin baya bayan nan, wadanda mafi akasari ke hawa kwale-kwale daga gabar ruwan Libya da na Tunisia.

Hukumr kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan hatsarin na daga cikin jerin irinsa da suka auku a tekun tun daga farkon watan Oktoba.

Hukumar ta ce ta samu rahoton cewa jirgin ruwan na dauke da mutane 120 cikinsu har da mata da kananan yara, inda ta kara da cewa an tsamo gawarwakin mutane 31 zuwa gabar tekun, har da ma 47 da suka tsallake rijiya da baya.

Hukumar ta ci gaba da cewa a cikin watanni 2 da suka gabata, akalla mutane 19, ciki har da mata da yara ne suka nutse a tekun a lokacin da kwale kwalen da suke ciki ya samu matsala a tsakiyar tekun Meditareniya.

Fiye da bakin haure dubu 20 ne suka mutu a cikin shekaru 7 da suka wuce a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.