Faransa zata taimakawa sabuwar gwamnatin Libya - Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana aniyar sa ta taimakawa sabuwar gwamnatin Libya a tattaunawar da suka yi da sabon Firaministan da aka zaba Abdel Hamid Dbeidah da shugaban kasa Mohammed Younes el-Menfi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Macron wanda ya taya shugabannin murnar nasarar da suka samu, ya jaddada matsayin Faransa na ganin an kawo karshen rikicin kasar da kuma fatar kasar tare da kasashen duniya ke da ita akan su.
Shugaban yace a shirye yake ya basu goyan baya wajen sauke nauyin dake kan su musamman sake hada kan kasar da hukumomin gwamnati wuri guda.
Kasashen Jamus da Italia da Faransa da Amurka da kuma Birtaniya sun bayyana cewar akwai aiki sosai a gaban sabbin shugabannin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu