Isa ga babban shafi

Faransa da kawayenta sun yi barazanar takunkumi ga masu katsalandan a rikicin Libya

Faransa, Italiya da Jamus sun ce a shirye suke su dauki matakin kakaba takunkumai kan dukkanin kasashen da suke katsalandan a rikicin kasar Libya, gami da karya dokar haramcin cinikin makamai da kasar da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kafa.

Motar dakarun gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.
Motar dakarun gwamnatin Libya da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita. © REUTERS/Ayman Al-Sahili
Talla

Sanawar dai bata ambaci sunan wata kasa da ake tuhuma da shiga rikicin na Libya ba.

Sai dai a bayyane take mayakan Janar Khalifa haftar da ke kokarin kifar da gwamnati na samun goyon bayan Rasha, Masar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa, yayinda Turkiya ke taimakawa gwamnatin hadin gwiwar da majalisar dinkin duniya ta amince da ita.

Da suke bayyana matukar damuwa game da yadda rikici ke dada rincabewa a Libya, kasashen Jamus, Faransa da Italiya sun bukaci bangarorin da ke rikici da juna da masu taimaka musu daga kasashen waje da su dakatar da rikicin.

Tun a shekarar 2015 rikicin shugabanci ya barke tsakanin gwamantin Libya dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, da dakarun tsohon Janar din sojin kasar Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.