Isa ga babban shafi

Turkiya ta gargadi dakarun Haftar kan yiwuwar kaiwa sojojinta farmaki a Libya

Turkiya ta sha alwashin daukar matakin soji a Libya, muddin rundunar mayakan Janar Khalifa Haftar mai iko da gabashin kasar ya kaiwa dakarunta farmaki.

Ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar
Ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar REUTERS/File Photo
Talla

Ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar ne yayi wannan gargadi yayin da ya ziyarci dakarun kasar dake birnin Tripoli.

A baya bayan nan Janar Khalifa Haftar ya sha alwashin kaddamar da farmaki kan sojojin kasashen ketaren da ya kira da ‘yan mamaya, sakamakon goyon bayan da suke baiwa gwamnatin kasar da majalisar dinkin duniya ke marawa baya.

A makon jiya Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta ficewar Sojojin haya da na kasashen ketare daga Libya, ciki har da Sojin Rasha wadanda Majalisar ke zargi da rura wutar rikicin kasar.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar yayin wani zaman sirri daya gudanar ta bidiyon Internet, ilahirin mambobinsa 15 sun amince da kudirin tilastawa sojojin ketaren su gaggauta ficewa daga kasar wadda ke ci gaba da fuskantar rikici tun bayan hambarar da gwamnatin Mu'ammar  Ghaddafi a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.