Isa ga babban shafi
Libya

'Yan Libya sun koka bayan mutuwar Gaddafi

'Yan kasar Libya sun yi bitar cika shekaru 10 da juyin-juya-halin kasar wanda ya kai ga kawar da shugaba Muammar Ghadafi daga karagar mulki da kuma jefa kasar cikin halin tahsin hankali, inda wasu daga cikinsu ke kokawa.

Moammar Gaddafi
Moammar Gaddafi
Talla

Yayin da wasu daga cikin 'yan kasar ke murna kan abin da suka kira nasarar samun yancin walwala a yammacin kasar, su kuwa mazauna gabashin kasar na nuna alhini ne kan halin da suka tsinci kansu a ciki.

Rikicin da ya biyo bayan kawar da Ghadafi daga karagar mulki ya haifar da kashe dubban mutane da kuma mayar da kasar daya daga cikin mafi hadarin rayuwa sakamakon yadda 'yan bindiga suka mamaye ta.

A makon jiya Majalisar Dinkin Duniya ta yi nasarar shirya taron zaben shugabannin rikon kwaryar da za su jagoranci kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.