Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram : Manoma na kauracewa gonakki a Borno

A dai-dai lokacin da rundunar sojin Nigeria ke ikirarin cewar tana samun gagarumar nasara a yakin da take yi da kungiyar Boko Haram, sai kuma ga dukan alamu wankin hula na shirin kaiwa dare. Domin manoma a garin Maiduguri na dari-darin zuwa gonakansu saboda yadda ‘yan Boko Haram ke kashe mutane tare da yin garkuwa da da wasu yayin da suke aiki a gonakkinsu.

Sojojin Najeriya sun tsaurara tsaro a hanyar Damboa bayan 'Yan Boko Haram sun kwace motoci masu dakon kayan abinci a Borno
Sojojin Najeriya sun tsaurara tsaro a hanyar Damboa bayan 'Yan Boko Haram sun kwace motoci masu dakon kayan abinci a Borno AFP
Talla

A cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan mutane da dama suka rasa rayukansu yayin da wasu suka bata, a irin wannan yanayi, inda ake danganta faruwar hakan akan ‘yan ta’addar Boko Haram. Wakilinmu a Maiduguri Bilyamin Yusuf ya aiko da rahoto daga Maiduguri.

02:59

Boko Haram : Manoma na kauracewa gonakki a Borno

Bilyaminu Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.