Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun kashe wasu manoma

Kungiyar Boko Haram da ke Najeriya ta kashe wasu manoma shida yayinda suke aiki a gonakinsu da ke kauyen jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Mayakan Boko Haram da aka yi musayarsu da 'yan matan sakandaren Chibok 82, yayinda da suke gaisawa da 'yan uwansu.
Mayakan Boko Haram da aka yi musayarsu da 'yan matan sakandaren Chibok 82, yayinda da suke gaisawa da 'yan uwansu. REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Jami’an tsaron sa kai, da ke taimakawa yakin da ake da Kungiyar ne suka tabbatar da kai harin a kauyen Amrawa, tare da bayyana yadda aka kwace gonakin manoman bayan aiwatar da yankan rago a kansu.

Ko a makon da ya gabata, sai da wani wanda ya yi ikirari daga cikin kwamandojin kungiyar da aka yi musayarsu da ‘yan matan Chibok ya fitar da sakon bidiyon, barazanar sabbin hare-hare.

Yayin zantawarsra da sashin hausa na RFI Manjo Yahya Shinko y ace kamata yayi gwamnatin Najeriya ta kara yin taka tsantsan da kuma daukar matakan da suka dace don zama cikin shirin magance dukkanin sabbin barazanar da mayakan boko haram ka iya yi, don nunawa duniya cewa har yanzu da sauran karfinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.