Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Najeriya: 'Yan matan Chibok da aka sako zasu koma karatu a watan Satumba

Gwamnatin Najeriya ta jadda matsayinta na cigaba da tattaunawar da zata taimaka wajen sako ragowar ‘yan matan sakandaren Chibok, da sauran mutanen da ke tsare a hannun kungiyar Boko Haram.

Wasu daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok 82 da kungiyar Boko Haram ta sako bayan tattaunawa da gwamnatin Najeriya da masu shiga tsakani.
Wasu daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok 82 da kungiyar Boko Haram ta sako bayan tattaunawa da gwamnatin Najeriya da masu shiga tsakani. REUTERS/Zanah Mustapha
Talla

Ministar kula da harkokin mata da cigaban al’ummah Aisha Alhassan ce ta bayyana matsayar yayin ganawar da tayi da manema labarai a garin Abuja.

Minstar ta ce kodaye gwamnati na cigaba da tattaunawa kan sako sauran ‘yanmatan da ke tsare, ba zata iya bayyana lokacin da za’a samu nasarar hakan ba.

Aisha Alhassan ta kara da cewa za’a yiwa baki dayan ‘yan mata 82 da aka sako binciken da ya shafi kwakwalwa, bayan kammala duba lafiyarsu da ake kan yi a yanzu, domin saukaka musu sake shiga cikin al’ummah. Ko da yake a cewar ministar da dama daga cikin ‘yanmatan basa son komawa garin Chibok saboda tuna abun da ya faru da su.

Ministar kula da harkokin matan, ta yi alkawarin cewa a watan Satumba mai zuwa baki dayan ‘yan matan da aka sako zasu koma makaranta, tare da koyon ilimin na’ura mai kwakwalwa da kuma sana’o’in hannu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.