Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram na hana isar da kayan agaji ga mabukata

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa sama da mutane miliyan biyu za su fuskanci matsanancin yunwa a arewa maso gabashin Najeriya sakamakon tarkon kungiyar Boko Haram da ke hana isar da kayan agaji ga mabukata.

Boko Haram na hana isar da kayan agaji ga 'Yan gudun hijira
Boko Haram na hana isar da kayan agaji ga 'Yan gudun hijira REUTERS
Talla

Boko Haram na kawo tarnaki ga kokarin isar da kayan agaji ga ‘yan gudun hijira, a cewar Denise Brown babbar jami’ar da ke kula da ayyukan jin kai a Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya.

Jami’ar ta ce akwai wasu yankuna da ke kan iyaka da Chad da Nijar wadanda jami’anta ke shakkun zuwa kai agaji saboda Boko Haram.

Hukumar samar da abincin ta ce tana bukatar kudi miliyan 230 na dalar Amurka tsakanin yanzu zuwa Oktoba domin yaki da yunwa a Najeriya.

Denise ta ce kusan mutane miliyan 20 ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen Najeriya da Yemen da Somalia da Sudan ta kudu da ke fama da rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.