Isa ga babban shafi
Italiya

Italiya ta kaddamar da sabon tsarin karbar ‘Yan cirani

Gwamnatin Italiya ta bayyana wasu jerin sabbin tsare tsare, domin rage kwararar ‘yan gudun hijira zuwa kasar. Sai dai kuma tsare tsaren sun kunshi batun iza keyar ‘yan gudun hijirar da gwamnati ta ki amincewa da bukatarsu ta neman mafaka zuwa kasashen da suka fito.

'Yan cirani da ke ratsa tekun Bahrum daga Afrika zuwa Turai
'Yan cirani da ke ratsa tekun Bahrum daga Afrika zuwa Turai © Susanne Friedel
Talla

Ministan cikin gidan Italiyan Marco Minniti ya ce ‘yan gudun hijirar da aka amince su sami mafaka a kasar Italiyan za su rika gudanar da ayyuka don kaucewa zaman kashe wando ko da kuwa ladan da za a biya su ba mai yawa ba ne.

Daga cikin ayyukan akwai kulawa da filayen ajiye ababen hawa da ayyukan jin-kai hukumar bada agaji ta Red Cross da kuma da koyar da harsunan kasashensu a makarantu.

Tuni dai aka fara aiwatar da sabbin tsare tsaren kan ‘yan gudun hijirar a birnin Belluno da ke arewacin Italiya.

Sai dai kuma wasu ‘Yan Italiya na adawa da matakin musamman dangane da ba ‘yan gudun hijirar ayyukan yi. Saboda da yadda kashi 40 na jama’ar kasar ke fama da rashin ayyukan yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.