Isa ga babban shafi
Italiya

'Yan cirani 100 sun nitse a tekun meditereniya

Kungiyar Agaji ta Doctors Without Borders ta ce wasu Karin baki 100 sun nitse a tekun meditereniya kwanaki biyu bayan hadarin da ya ritsa da mutane 340.

An tabbatar da mutuwar baki 100 a teku.
An tabbatar da mutuwar baki 100 a teku. Facebook/Proactiva Open Arms
Talla

Kungiyar ta ce wasu mutane 27 da aka ceto daga cikin wadanda kwale-kwalen su ya nitse suka bada adadin a gabar ruwan Italia.

Wadanda suka tsiran sun ce sun taso ne daga bakin tekun Tripoli dake kasar Libya amma sai wadanda suka dauki nauyin tsallakawa da su suka shiga wani karamin kwale-kwale suka gudu suka bar su a tsakiyar teku.

Dubban mutane daga kasashen Africa musanman wadanda ke fama da rikice-rikicen yaki ne ke yunkurin shiga turai a bulaguron da ke tattare da hadurran gaske.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.