Isa ga babban shafi
Turai

Sanyi da kankara na halakar da 'Yan ci-rani a Turai

Hukumomin kasashen Turai sun bayyana cewa, akalla mutane 23 yawancinsu bakin haure ne suka rasa rayukansu a cikin kwanaki biyu, sakamakon tsananin sanyi da kankara da ake makawa a kasashen nahiyar.

Ana maka sanyi a Turai
Ana maka sanyi a Turai Reuters
Talla

Kasar Rasha ta gudanar da bikin Kirismati a cikin tsananin sanyin da ba ta taba ganin irinsa ba a cikin shekaru 120 da suka gabata, yayin da dusar kankara ta mamaye daukacin birnin Santanbul na Turkiya.

Mutane 10 daga cikin mamatan na baya-bayan nan, sun gamu da ajalinsu ne a Poland, in da a ranakun Juma’a da Asabar aka samu mutuwar mutane 10.

Sanyin ya lakume rayukan mutane bakwai cikin sa’oi 48 a Italiya, da suka hada da marasa gidajen kwana 5.

Dusar kankarar ta kuma tilasta wa hukumomin Italiya daukan matakin rufe filayen jiragen saman kasar guda uku a karshen mako.

Kazalika mutane uku ne suka mutu saboda sanyin da aka tafka a Jamhuriyar Czech da suka hada da marasa gidajen kwana guda biyu da kuma wani mai gadin motoci guda.

Hakama a Bulgaria sanyin ya daskarar da jikkunan ‘yan gudun hijirar Iraqi biyu da aka samu gawarwakinsu a wani yankin tsaunuka da ke kusa da kan iyakar Turkiya.

Tuni dai kasar Girka da ta karbi bakin haure fiye da dubu 60, ta sauya wa wasu bakin wuraren zama masu dumi saboda tsanannin sanyin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.