Isa ga babban shafi
Jamus-Girka

Jamus za ta mayar da 'yan ci-rani Girka

Kasar Jamus ta ce daga watan Mayun shekara 2017, za ta dawo da shirin mayar da sabbin 'yan gudun hijira da suka shiga kasar zuwa Girka, bayan shafe shekaru 5 da dakatar da shirin sakamakon rashin kyawun yanayi a sansanonin Girka.

Sanyin hunturu ya addabi 'Yan ci-rani a Kasashen Turai
Sanyin hunturu ya addabi 'Yan ci-rani a Kasashen Turai Foto: AFP
Talla

Cikin tsohon tsarin da ake kira da ''Dublin'' dole ne 'yan gudun hijira su fara neman mafaka a kasar da suka fara shiga, da suka hadar da Italiya da Bulgaria da kuma ita kan ta Girka da masu gudun hijirar suka fi tururuwa.

To sai dai kuma Girka ta soki matakin na Jamus inda ta ce, hakan zai dora nauyi matuka kan kasashen da 'yan gudun hijirar suka fara isa.

Yanzu haka dai akwai akalla 'yan gudun hijira kimanin 62,000 da ke kasar ta Girka, babu kuma ranar barinsu kasar sakamakon rufe iyakoki da kasashen da ke makwabtaka da ita suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.