Isa ga babban shafi
Nijar

Ana tsare da daruruwan ‘Yan Boko Haram a Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar ta ce akwai ‘yan Boko Haram sama da dubu daya da ake tsare da su a sassa daban daban na kasar, kuma za a fara yi masu shara’a nan ba da jimawa ba, kamar dai yadda ministan cikin gidan kasar Bazoum Mohammad ya tabbatar.

Mohamed Bazoum ministan cikin gidan Nijar a ziyarar da ya kai yankin Diffa
Mohamed Bazoum ministan cikin gidan Nijar a ziyarar da ya kai yankin Diffa ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Bazoum ya ce tuni aka nada alkalan da za su gudanar da bincike dangane da irin laifufukan da ake zarginsu da aikatawa.

Ministan ya ce alkalan za su yi tattaki har zuwa cikin kauyukan jihar Diffa inda aka kama wadanda ake zargin domin gudanar da bincike, wanda hakan zai bayar da dama yi ma su shara’a a cikin gaggauwa.

Majiyoyin tsaro a jamhuriyar ta Nijar sun tabbatar da cewa akwai ‘yan Boko Haram dubu daya da 200 da suka hada da ‘yan Nijar da kuma ‘yan Najeriya da jami’an tsaron suka kama, wasu a fagen daga yayin da wasu aka kama su lokacin da ake sintiri karkashin dokar ta-baci da aka kafa a yankin.

Sai dai a cewar Mista Bazoum, bayan gudanar da bincike, wadanda aka gano cewa laifufukansu ba su taka kara sun karya ba za a sake su nan take, yayin da sauran za su gurfana a gaban kotu domin yi masu hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.