Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Hukumomin Nijar zasu gabatar da yan Boko Haram zuwa Kotu

A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun sanar da gaggauta gabatar da mayakan boko haram da ake tsare da su kusan shekara daya ga alkalan kotun .

Shugaban sashin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban sashin kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP/Capture d'écran vidéo
Talla

Ministan cikin gidan kasar Bazoum Mohamed da ya halarci a farkon makon nan wani gangami a jihar Diffa ida aka bayyana cewa wasu mayakan boko haram sun mika wuya zuwa hukumomin kasar ne ya sanar da wannan matsaya da hukumomin Nijar suka cimma.

Wata majiya daga ofishin tsaron Nijar na nuni da cewa kusan mayakan boko haram 1200 ake tsare da su da kuma suka hada da yan Nijar da yan Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.