Isa ga babban shafi
DRC

DR Congo ta umarci rufe hanyoyin Sadarwa

Hukumomin Jamhuriyar Dimokiradiyar congo sun bada umurnin rufe hanyoyin sadarwar da suka hada da Facebook da kuma Whatsapp kwanaki biyar kafin karewar wa’adin mulkin shugaban kasar Joseph Kabila.

Shugaba DR Congo Joseph Kabila.
Shugaba DR Congo Joseph Kabila. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Hukumar kula da sadarwar kasar ta gabatar da umurnin ga daukacin kamfanonin sadarwa dan kaucewa fargabar tashin hankalin da ake yi a kasar.

A ranar 20 ga watan nan ne wa’adin shugaba Kabila ke karewa, amma gwamnatin kasar ta kasa gudanar da zabe saboda yadda 'yan adawa suka bayyana rashin amincewar su da takarar Kabila wanda ya kamala wa’adi na biyu.

Hukumar zaben ta ce sai shekarar 2018 a gudanar da zabe, yayin da 'yan adawar ke cewa ba za su amince shugaba Kabila ya kara kwana guda daga ranar 20 ga watan nan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.