Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

‘Yan adawar Congo sun kaddamar da yakin ban-kwana da Kabila

Jam’iyyun adawar Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun kaddamar da wani kamfen na bankwana ga shugaban kasar Joseph Kabila da wa’adin sa ke karewa ranar 20 ga watan gobe.

Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Joseph Kabila
Shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Joseph Kabila REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Kamfe din mai taken ‘Bye Bye Kabila’ na bukatar ganin shugaban ya sauka daga mukamin sa ne da zaran wa’adin shi ya kare, bayan ya kasa gudanar da zaben shugaban kasa.

Yayin wani gangami da aka gudanar a birnin Kinshasa, daya daga cikin wadanda suka shirya taron Merve Gozo, ya ce suna amfani da wanann dama ce domin shaidawa duniya cewar lokacin saukar shugaban Joseph Kabila ya yi, domin ba su bukatar ci gaba da zaman sa a karagar mulki.

Mista Gozo ya ce za su gudanar da zanga-zangar lumana ranar Juma’a mai zuwa don shaidawa shugaban cewar ya dace ya sanya sunansa cikin tarihi wajen mika mulki ba tare da samun tashin hankali ba.

Shugaba Kabila ya hau karagar mulki ne bayan kashe mahaifinsa Laurent-Desire Kabila da wani dogarin shiya yi a shekarar 2001, kafin daga bisani ya tsaya takarar zabe a shekarar 2006 da 2011 wanda ya yi nasara.

Kundin tsarin mulkin kasar ya hana shi takarar wa’adi na uku, amma shugaban ya ki amincewa, inda aka dage zaben zuwa shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.