Isa ga babban shafi
Najeriya

Iyayen ‘Yan Matan Chibok sun bukaci Buhari ya yi murabus

Iyayen ‘Yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace sun bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka daga kujerarsa tun da ba zai iya ceto ‘ya’yansu ba da ake garkuwa da su sama da shekara biyu.

Jami'an tsaro sun hanawa iyayen matan Chibok ganin Shugaba Muhammadu Buhari
Jami'an tsaro sun hanawa iyayen matan Chibok ganin Shugaba Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin gudanar da wata zanga zanga jiya Alhamis, wasu daga cikin iyayen sun soki shugaban na Najeriya da karya alkawalin da ya dauka kafin zabe.

Iyayen sun zargi Buhari da fita batun ‘yayansu da ke ci gaba da rayuwa ahannun ‘yan ta’adda.

Daya daga cikin iyayen ‘Yan Matan na Chibok, Enoch Mark, wanda aka sace ‘yayansa biyu ya ce sun zabi Buhari ne saboda alkawarin da ya yi kafin zabe na ceto ‘ya’yansu.

A ranar 14 ga Afrilun 2014 ne Mayakan Boko Haram suka abkawa makarantar garin Chibok suka sace ‘Yan Matan sama da 200.

Hankalin iyayen matan dai ya kara tashi ne bayan Kungiyar Boko Haram ta fitar da hoton bidiyon da ya nuna wasu daga cikin ‘Yan Matan na Chibok da suke ci gaba da garkuwa da su.

Hoton Bidiyon da Boko Haram ta fitar ya kara jefa iyayen Matan Chibok cikin mawuyacin hali
Hoton Bidiyon da Boko Haram ta fitar ya kara jefa iyayen Matan Chibok cikin mawuyacin hali REUTERS

Daga cikin ‘Yan matan da Boko Haram ta nuna a bidiyon ta bukaci iyayensu su roki gwamnati ta amince da bukatun Boko Haram domin ganin an sake su.

Kungiyar Boko Haram ta bukaci gwamnati ne ta saki mabobinta da ake tsare da su kafin sakin ‘Yan matan na Chibok.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.