Isa ga babban shafi
Dr Congo

Jami'an tsaro sun bude wuta kan masu zanga zanga

Mutum guda ya rasa ransa bayan ‘Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga zanga domin tarwatsa su a garin Beni da ke gabashin Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo inda aka kashe fararen hula 51 a satin da ya gabata.

Masu zanga zanga a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo
Masu zanga zanga a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo KUDRA MALIRO / AFP
Talla

A farkon satin da muke ciki aka kara yawan jami’an tsaro a manyan hanyoyin garin na Beni bayan taron da masu zanga zangar suke saboda alhinin kashe fararen hula 51.

Dandazon mutane dake kona tutocin jam’iyya mai mulkin kasar sun zargi gwamnatin Janhuriyyar Congon karkashin Jooseph Kabila da gazawa wajen tsare rayukan mutane a yankin.

Daga shekara ta 2014 zuwa yanzu sama da mutane 650 aka kashe a ciki da wajen Beni, kashe kashen da gwamnatin kasar ke zargin kungiyar ‘yan tawayen ADF da aikatawa, wadda ke da tushe a kasar Uganda.

A baya an sha zargin mayakan na ADF da cin zarafin da’Adam baya ga fasa kaurin kayayyaki da kuma sata da yi garkuwa da mutane.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.