Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Demokradiyar Congo

‘Yan sanda sunyi arangama da masu zanga-zanga a Congo

‘Yan sanda a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma ruwan zafi domin tarwatsa zanga-zangar da ‘yan adawa suka shirya a birnin Kinshasa da kuma wasu yankuna na kasar.

Masu zanga-zanga a Congo
Masu zanga-zanga a Congo REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Dubu dubatar masu adawa da shugaban kasar ta Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo Joseph Kabila ne suka halarci zanga-zangar da aka gudanar a birnin Kinshasa inda suke neman a gudanar da zaben shugabancin kasar kafin ranar 19 ga wannan disambar bana, wanda shi ne karshen wa’adin mulkin Kabila.

Jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma motocin ruwan zafi domin tarwatsa gungun ‘yan adawar ne, a daidai lokacin masu zanga-zangar suka kaucewa hanyoyin da hukumomin birnin suka ba su izinin ratsawa a lokacin tattakin nasu.

A garin Lubumbashi ne wanda shi ne cibiyar sabon jagoran ‘yan adawar kasar Moise Katumbi, an yi irin wannan zanga-zanga, duk da cewa dan adawar ya fice daga kasar, yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce wasu dubban mutanen sun fito a  kan titunan birnin Goma da ke yankin Kivu.

Wasu daga cikin manyan bukatun ‘yan adawar sun hada da soke wani kudurin doka da kotun kolin kasar ta fitar, wanda ke bai wa Joseph Kabila damar sake tsayawa takara duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya haramta ma sa hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.