Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Simone Gbagbo ta yi zargin yunkurin yi mata fyade

Matar Tsohon shugaban kasar Cote d’Ivoire Simone Gbagbo ta ki amincewa da tuhumar da ake ma ta na cin zarafin Bil Adama a rikicin siyasar kasar na shekarar 2010, inda ta yi zargin cewar an yi kokarin yi mata fyade lokacin da ake tsare da ita.

Simone Gbagbo Matar tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo
Simone Gbagbo Matar tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Misis Gbagbo tace ana tuhumar ta ne akan laifin da ba ta aikata ba domin neman bata ma ta suna.

Matar tsohon shugaban kasar ta kuma ce sojojin Faransa da ke kasar sun dauki hoto lokacin da ake kokarin yi mata fyade bayan kamata da mijinta a ranar 11 ga watan Aprilun shekarar 2011.

Ana tuhumar matar tsohon shugaban ne da laifin shirya gangamin keta hakkin bil’adama akan magoya bayan mai adawa da takarar Mijinta Alassane Ouattara a lokacin da mijinta ya ki amincewa da shan kaye a zaben 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.