Isa ga babban shafi
COTE D'IVOIRE

Ouattara ya ce ba zai sake mika dan kasar shi ICC ba

Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara yace ba zai sake mika wani dan kasar shi ba zuwa kotun hukunta manyan laifuka ta ICC dake Birnin Hague, inda tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ke fuskantar shari’a kan zargin aikata laifukan yaki a rikicin siyasar da ya biyo bayan zaben 2010.

Alassane Ouattara Shugaban Kasar Cote D'ivoire
Alassane Ouattara Shugaban Kasar Cote D'ivoire RFI/Pierre René-Worms
Talla

Mista Ouattara ya fadi haka ne a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Faransa Francois Hollande a Paris.

Kuma a cewarsa yanzu kasar Cote d’Voire na da cikakken tsarin shari’a da za a iya gurfanar da mutanen kasar.

Sama da mutane 3,000 dai suka mutu a rikicin da aka shafe watanni 5 ana yi a Cote d’Ivoire saboda Gbagbo ya ki sauka kan karagar mulki bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.