Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire-ICC

An soma Shari’ar Gbagbo a Kotun ICC

A yau Alhamis kotun ICC da ke hukunta laifukan yaki ta duniya da ke birnin Hague ta soma shari’ar tsohon shugaba Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo, wanda ake zargi da tayar da rikiciin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu uku a lokacin rikicin zaben kasar na shekara ta 2010.

Kotun ICC za ta fara shari'ar Charles Blé Goudé da Laurent Gbagbo
Kotun ICC za ta fara shari'ar Charles Blé Goudé da Laurent Gbagbo AFP PHOTO/ SIA KAMBOU
Talla

Gbagbo ya kasance shugaban kasa na farko da ya gurfana gaban kotun ICC, inda wasu mutanen Afrika ke zargin Kotun da farautar shugabannin Afrika kawai.

Tun kafa ta a 2002 domin hukunta laifukan yaki, kotun ta mayar da hankali a Afrika kamar yadda ta kaddamar da bincike a kasashen Sudan da Libya da Uganda da Mali da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Cote d’Ivoire da Jamhuriyar Dimokuradiyar Congo.

Wasu shugabannin Afrika sun zargin kotun a matsayin kare farautar kasashen yammaci.

Amma da dadewa Kotun na kare kanta inda Babbar mai gabatar da kara a kotun Fatou Bensouda ‘yar kasar Gambia a Nahiyar Afrika ke cewa da bukatun kasashen ne kotun ke aiki.

Ana dai zargin Laurent Gbagbo ne da aikata laifukan yaki a rikicin siyasar da ya faru a Cote d’Ivoire bayan ya ki amincewa da shan kaye a zaben 2010.

Gbagbo zai gurfana ne a gaban kotun tare da Charles Ble Goude babban kwamandansa.

Baya ga Gbagbo, akwai Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir da Kotun ICC ta bayar da sammacin kamo shi kan rikicin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.